Far 46:32-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. mutanen kuwa makiyaya ne, sun kuwa zo da garkunansu na awaki da na tumaki, da garkunansu na shanu, da dukkan abin da suke da shi.’

33. To, sa'ad da Fir'auna zai kira ku, ya tambaye ku, ‘Mece ce sana'arku?’

34. Sai ku ce, ‘Ranka ya daɗe, mu makiyayan shanu ne tun muna 'yan yara har zuwa yau, da mu da kakanninmu,’ don ku sami wurin zama a ƙasar Goshen, gama kowane makiyayi abin ƙyama ne ga Masarawa.”

Far 46