Yusufu ya shiga ya yi magana da Fir'auna, ya ce, “Mahaifina da 'yan'uwana, da garkunansu na awaki da na tumaki, da garkunan shanu, da dukan abin da suka mallaka, sun zo daga ƙasar Kan'ana, yanzu suna ƙasar Goshen.”