Far 44:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yusufu ya umarci mai hidimar gidansa, ya ce, “Cika tayakan mutanen nan da abinci iyakar yadda za su iya ɗauka, ka kuma sa kuɗin kowanne a bakin taikinsa,

2. ka sa finjalina na azurfa a bakin taikin autan, tare da kuɗinsa na hatsin.” Sai ya yi kamar yadda Yusufu ya faɗa masa.

Far 44