Far 41:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan shekaru biyu cif, Fir'auna ma ya yi mafarki, ga shi, yana tsaye a bakin kogin Nilu,

2. sai ga shanu bakwai masu ƙiba mulmul suka fito daga Nilu, suka yi kiwo cikin iwa.

3. Ga kuma waɗansu shanu bakwai munana ramammu suka fito daga cikin Nilu a bayansu, suka tsaya kusa da waɗancan shanu a bakin Nilu.

4. Sai shanun nan munana ramammu suka cinye shanun nan bakwai masu sheƙi, masu ƙibar. Sai Fir'auna ya farka.

5. Barci kuma ya kwashe shi, ya sāke yin mafarki a karo na biyu, sai zangarku bakwai masu kauri kyawawa suna girma a kara gudu.

6. Ga shi kuma, a bayansu waɗansu zangarku bakwai suka fito sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar.

7. Sai siraran zangarkun suka haɗiye zangarkun nan bakwai masu kauri kyawawa. Sai Fir'auna ya farka, ashe, mafarki ne.

8. Saboda haka da safe, hankalinsa ya tashi, sai ya aika aka kirawo dukan bokayen Masar da dukan masu hikimar Masar, Fir'auna kuwa ya faɗa musu mafarkansa, amma ba wanda ya iya fassara masa su.

9. Sai shugaban masu shayarwa ya ce wa Fir'auna, “Yau, na tuna da laifofina.

10. Sa'ad da ka yi fushi da barorinka, ka sa ni da shugaban masu tuya cikin kurkukun da yake a cikin gidan shugaban masu tsaron fāda,

11. muka yi mafarki dare ɗaya, ni da shi, kowane mutum da irin tasa fassarar mafarkin.

12. Akwai wani Ba'ibrane, ɗan saurayi, tare da mu, bawan shugaban masu tsaron fāda, sa'ad da muka faɗa masa sai ya fassara mana mafarkanmu, ya yi wa kowannenmu fassara bisa kan mafarkinsa.

13. Yadda ya fassara mana haka kuwa ya zama, aka komar da ni matsayina, mai tuya kuwa aka rataye shi.”

Far 41