Far 40:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan waɗannan al'amura, sai mai shayarwa da mai tuya na Sarkin Masar suka yi wa maigidansu Sarkin Masar laifi.

2. Fir'auna ya yi fushi da ma'aikatan nan nasa biyu, wato shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya.

3. Ya ba da su a sa su kurkuku, cikin gidan shugaban masu tsaron fāda, wato kurkuku inda Yusufu yake a tsare.

4. Shugaban 'yan tsaron ya danƙa su ga Yusufu don ya hidimta musu, sun kuwa jima a kurkukun har an daɗe.

5. Suka yi mafarki, su biyu ɗin, a dare ɗaya, da shi mai shayarwar da mai tuyar na gidan Sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, kowanne kuwa da nasa mafarkin da kuma tasa irin fassarar mafarkin.

6. Da Yusufu ya zo wurinsu da safe, ya ga sun damu.

7. Sai ya tambaye su ya ce, “Me ya sa fuskokinku suke a yamutse yau?”

8. Suka ce masa, “Mafarkai muka yi, ba kuma wanda zai fassara mana su.”Sai Yusufu ya ce musu, “Ashe, ba a wurin Allah fassarori suke ba? Ku faɗa mini su, ina roƙonku.”

9. Saboda haka, shugaban masu shayarwa ya faɗa wa Yusufu mafarkinsa, ya ce masa, “A mafarkina ga kurangar inabi a gabana.

10. A kurangar akwai rassa uku. Sai ta yi toho, ta huda nan da nan, ta kuma yi nonna, har suka nuna suka zama inabi.

Far 40