27. Waɗannan su ne 'ya'yan Ezer, maza, Bilhan, da Zayawan, da Akan.
28. Waɗannan su ne 'ya'yan Dishan, maza, Uz da Aran.
29. Waɗannan su ne shugabannin Horiyawa, shugaba Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana,
30. da Dishon, da Ezer, da Dishan, waɗannan su ne shugabannin Horiyawa bisa ga shugabancinsu a ƙasar Seyir.
31. Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a ƙasar Edom, kafin wani sarki ya taɓa yin mulkin Isra'ilawa.
32. Bela ɗan Beyor ya yi sarautar Edom, sunan birninsa kuwa Dinhaba.
33. Bela ya rasu, sai Yobab ɗan Zera daga Bozara ya ci sarauta a bayansa.
34. Ɗan Yobab ya rasu, sai Husham na ƙasar Temanawa ya ci sarauta a bayansa.
35. Da Husham ya rasu, sai Hadad ɗan Bedad wanda ya ci Madayana a ƙasar Mowab, ya ci sarauta a bayansa, sunan birninsa kuwa Awit ne.
36. Da Hadad ya rasu, sai Samla na Masreka ya ci sarauta a bayansa.
37. Da Samla ya rasu, sai Shawul na Rehobot ta Yufiretis ya ci sarauta a bayansa.
38. Da Shawul ya rasu, sai Ba'al-hanan ɗan Akbor ya ci sarauta a bayansa.
39. Da Ba'al-hanan ɗan Akbor ya rasu, sai Hadad ya ci sarauta a bayansa, sunan birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel 'yar Matred, 'yar Mezahab.
40. Waɗannan su ne sunayen sarakunan Isuwa bisa ga dangoginsu da bisa ga wurin zamansu. Ga sunayensu, sarki Timna, da Alwa, da Yetet,
41. da Oholibama, da Ila, da Finon,
42. da Kenaz, da Teman, da Mibzar,
43. da Magdiyel, da Iram. Waɗannan su ne sarakunan Edom, (wato Isuwa ne kakan Edomawa) bisa ga wuraren zamansu a ƙasar mallakarsu.