11. 'Ya'yan Elifaz su ne Teman, da Omar, da Zeho, da Gatam, da Kenaz.
12. Timna kuwa ƙwarƙwarar Elifaz ɗan Isuwa ce, ta haifa wa Elifaz Amalek. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Ada, matar Isuwa.
13. Waɗannan su ne 'ya'yan Reyuwel, maza, Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Basemat, matar Isuwa.
14. Waɗannan su ne 'ya'yan Oholibama matar Isuwa 'yar Ana ɗan Zibeyon. Ta haifi wa Isuwa Yewush, da Yalam, da Kora.
15. Waɗannan su ne shugabanni na zuriyar Isuwa. Ga 'ya'yan Elifaz, maza, ɗan farin Isuwa, shugaba Teman, da Omar, da Zeho, da Kenaz,
16. da Kora, da Gatam, da Amalek, su ne shugabannin Elifaz cikin ƙasar Edom, su ne 'ya'yan Ada.
17. Waɗannan su ne 'ya'yan Reyuwel, maza, ɗan Isuwa. Shugaba Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza, waɗannan su ne shugabannin Reyuwel na cikin ƙasar Edom, su ne 'ya'ya maza na Basemat, matar Isuwa.
18. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Oholibama matar Isuwa, shugaba Yewush, da Yalam, da Kora, waɗannan su ne shugabanni waɗanda Oholibama matar Isuwa, 'yar Ana ta haifa.
19. Waɗannan su ne 'ya'yan Isuwa, maza, wato Edom, da shugabanninsu.
20. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Seyir Bahore, mazaunan ƙasar Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana,
21. da Dishon, da Ezer, da Dishan. Waɗannan su ne shugabannin Horiyawa, 'ya'yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.
22. 'Ya'yan Lotan, maza, su ne Hori da Hemam, 'yar'uwarsa Timna ce.
23. Waɗannan su ne 'ya'yan Shobal, maza, Alwan, da Manahat, da Ebal, da Sheho, da Onam.
24. Waɗannan su ne 'ya'yan Zibeyon, maza, Aiya da Ana. Shi ne Ana wanda ya sami maɓuɓɓugan ruwan zafi a cikin jeji, a sa'ad da yake kiwon jakunan mahaifinsa Zibeyon.
25. Waɗannan su ne 'ya'yan Ana, Dishon da Oholibama 'yar Ana.