19. Saurayin kuwa bai yi jinkirin aikata batun ba, gama yana jin daɗin 'yar Yakubu. Shekem kuwa shi ne aka fi darajantawa a cikin gidan.
20. Hamor kuwa da ɗansa Shekem, suka je dandali a bakin ƙofar birni, suka yi wa mutanen birninsu magana, suka ce,
21. “Waɗannan mutane suna abuta da mu, ai, sai su zauna a ƙasar a sake, gama ga shi akwai isasshen fili a ƙasar dominsu. Bari mu auri 'ya'yansu mata, mu kuma mu aurar musu da 'ya'yanmu mata.
22. Ga sharaɗin da mutanen za su yarda su zauna tare da mu, mu zama jama'a ɗaya, wato kowane namiji a cikinmu ya yi kaciya kamar yadda su suke da kaciya.
23. Da shanunsu, da dukiyarsu da dukan dabbobinsu, ashe, ba za su zama namu ba? Bari dai kurum mu yarda da su, su zauna tare da mu.”
24. Duk jama'ar birnin suka yarda da maganar Hamor da ɗansa Shekem. Aka kuwa yi wa kowane namiji kaciya.
25. A rana ta uku, sa'ad da jikunansu suka yi tsami, biyu daga cikin 'ya'yan Yakubu, Saminu da Lawi, 'yan'uwan Dinatu, suka ɗauki takubansu suka fāɗa wa birnin ba labari, suka karkashe mazajen duka.
26. Suka kashe Hamor da ɗansa Shekem da takobi, suka ɗauko Dinatu daga gidan Shekem suka yi tafiyarsu.
27. 'Ya'yan Yakubu kuwa suka tarar da kisassun, suka washe birnin, saboda sun ɓata 'yar'uwarsu.
28. Suka kwashe garkunan awaki da tumaki, da garkunan shanu da jakunansu da dukan abin da yake cikin birnin da na cikin saura,
29. dukan dukiyarsu, da 'yan ƙananansu, da matansu, wato dukan abin da yake cikin gidajen, suka kwashe.
30. Sai Yakubu ya ce wa Saminu da Lawi, “Kun jawo mini wahala. Kun sa na zama abin ƙi ga Kan'aniyawa da Ferizziyawa mazaunan ƙasar. Mutanena kima ne, in suka haɗa kai suka fāɗa mini, za su hallaka ni, da ni da gidana.”
31. Amma 'ya'yansa suka ce, “Zai mai da ƙanwarmu kamar karuwa?”