Far 34:19-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Saurayin kuwa bai yi jinkirin aikata batun ba, gama yana jin daɗin 'yar Yakubu. Shekem kuwa shi ne aka fi darajantawa a cikin gidan.

20. Hamor kuwa da ɗansa Shekem, suka je dandali a bakin ƙofar birni, suka yi wa mutanen birninsu magana, suka ce,

21. “Waɗannan mutane suna abuta da mu, ai, sai su zauna a ƙasar a sake, gama ga shi akwai isasshen fili a ƙasar dominsu. Bari mu auri 'ya'yansu mata, mu kuma mu aurar musu da 'ya'yanmu mata.

22. Ga sharaɗin da mutanen za su yarda su zauna tare da mu, mu zama jama'a ɗaya, wato kowane namiji a cikinmu ya yi kaciya kamar yadda su suke da kaciya.

23. Da shanunsu, da dukiyarsu da dukan dabbobinsu, ashe, ba za su zama namu ba? Bari dai kurum mu yarda da su, su zauna tare da mu.”

24. Duk jama'ar birnin suka yarda da maganar Hamor da ɗansa Shekem. Aka kuwa yi wa kowane namiji kaciya.

25. A rana ta uku, sa'ad da jikunansu suka yi tsami, biyu daga cikin 'ya'yan Yakubu, Saminu da Lawi, 'yan'uwan Dinatu, suka ɗauki takubansu suka fāɗa wa birnin ba labari, suka karkashe mazajen duka.

26. Suka kashe Hamor da ɗansa Shekem da takobi, suka ɗauko Dinatu daga gidan Shekem suka yi tafiyarsu.

27. 'Ya'yan Yakubu kuwa suka tarar da kisassun, suka washe birnin, saboda sun ɓata 'yar'uwarsu.

Far 34