1. Yanzu fa Dinatu 'yar Lai'atu, wadda ta haifa wa Yakubu, ta fita ta ziyarci waɗansu matan ƙasar,
2. sai Shekem, ɗan Hamor Bahiwiye, yariman ƙasar, da ya gan ta, ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta.
3. Ransa kuwa ya zaƙu da son Dinatu 'yar Yakubu. Ya ƙaunaci budurwar, ya kalallame ta da maganganu masu daɗi.
4. Sai Shekem ya yi magana da mahaifinsa, Hamor, ya ce, “Ka auro mini wannan budurwa ta zama matata.”
5. Yakubu kuwa ya ji an ɓata 'yarsa, Dinatu, amma 'ya'yansa maza suna tare da garken cikin saura, saboda haka Yakubu ya yi shiru har kafin su komo.