Far 33:18-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Yakubu kuwa ya kai birnin Shalem wanda yake ƙasar Kan'ana lafiya, a kan hanyarsa daga Fadan-aram, ya kuwa yi zango a ƙofar birnin.

19. Ya kuma sayi yankin saura inda ya kafa alfarwarsa daga 'ya'yan Hamor, mahaifin Shekem, a bakin azurfa ɗari.

20. A wurin ya gina bagade ya sa masa suna El-Elohe-Isra-el.

Far 33