Far 30:2-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Fushin Yakubu ya yi ƙuna a kan Rahila, ya ce, “Ina daidai da Allah ne, wanda ya hana ki haihuwa?.”

3. Sai ta ce, “Ga kuyangata Bilha, ka shiga wurinta, domin ta haihu bisa gwiwoyina, domin ni ma in sami 'ya'ya ta wurinta.”

4. Don haka ta ba shi Bilha ta zama matarsa. Yakubu kuwa ya shiga wurinta.

5. Bilha kuwa ta yi ciki, ta haifa wa Yakubu ɗa.

6. Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni, ya ji muryata, ya kuwa ba ni ɗa.” Saboda haka ta raɗa masa suna Dan.

7. Bilha, kuyangar Rahila, ta sāke yin ciki, ta haifa wa Yakubu ɗa na biyu.

8. Sai Rahila ta ce, “Da gawurtacciyar kokawa na yi kokawa da 'yar'uwata, har na yi rinjaye,” sai ta raɗa masa suna Naftali.

9. Sa'ad da Lai'atu ta ga ta daina haihuwa, sai ta ɗauki kuyangarta Zilfa, ta ba Yakubu ta zama matarsa.

10. Kuyangar Lai'atu, Zilfa, ta haifa wa Yakubu ɗa.

11. Lai'atu kuma ta ce, “Sa'a!” Saboda haka ta sa masa suna Gad.

12. Kuyangar Lai'atu ta sāke haifa wa Yakubu ɗa na biyu.

13. Lai'atu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Gama mata za su ce da ni mai farin ciki,” saboda haka ta raɗa masa suna Ashiru.

14. A kwanakin kakar alkama, Ra'ubainu ya fita ya samo manta uwa a saura, ya kawo wa mahaifiyarsa Lai'atu. Sai Rahila ta ce wa Lai'atu, “Ina roƙonki, ɗiba mini daga cikin manta uwar da ɗanki ya samo.”

15. Amma ta ce mata, “Kanƙanen abu ne da kika ƙwace mini mijina? Za ki kuma ƙwace manta uwar da ɗana ya samo kuma?”Rahila ta ce, “To, in haka ne, bari ya kwana tare da ke a daren yau a maimakon manta uwar da ɗanki ya samo.”

Far 30