Far 18:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuwa ya bayyana ga Ibrahim kusa da itatuwan oak na Mamre, a lokacin da yake zaune a ƙofar alfarwarsa da tsakar rana.

2. Da ya ɗaga idonsa, ya duba sai ga mutum uku suna tsaye a gabansa. Da ya gan su, sai ya sheƙa da gudu daga ƙofar alfarwar, don ya tarye su. Ya yi ruku'u,

3. ya ce, “Ya Ubangiji, in na sami tagomashi a gabanka, kada ka wuce gidana. A shirye nake in yi muku hidima.

4. Bari a kawo ɗan ruwa ku wanke ƙafafunku, ku shaƙata a gindin itace,

Far 18