Far 17:2-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Zan yi maka alkawari, in ba ka zuriya mai yawa.”

3. Sai Abram ya yi ruku'u, Allah kuwa ya ce masa,

4. “Wannan shi ne alkawarin da zan yi maka, za ka zama uba ga al'ummai masu ɗumbun yawa.

5. Ba za a ƙara kiran sunanka Abram ba, amma sunanka zai zama Ibrahim, gama na sa ka, ka zama uba ga al'ummai masu ɗumbun yawa.

6. Zan arzuta ka ainun, daga gare ka zan yi al'ummai, daga gare ka kuma sarakuna za su fito.

7. “Zan kafa alkawarina da kai, da zuriyarka a bayanka cikin dukan tsararrakinsu, madawwamin alkawari ke nan, in zama Allahnka da na zuriyarka a bayanka.

8. Zan ba ka, kai da zuriyarka a bayanka, ƙasar baƙuncinka, wato dukan ƙasar Kan'ana ta zama mallakarka har abada, ni kuwa zan zama Allahnsu.”

9. Allah kuma ya ce wa Ibrahim, “Kai fa, sai ka kiyaye alkawarina, da kai da zuriyarka a bayanka cikin dukan tsararrakinsu.

10. Wannan shi ne alkawarina da za ka kiyaye, da kai da zuriyarka a bayanka. Sai a yi wa kowane ɗa namiji kaciya.

11. Loɓarku za ku yanke, don alamar alkawari a tsakanina da ku.

Far 17