10. Akwai ramummukan kalo da yawa a kwarin Siddim. Da Sarkin Saduma da na Gwamrata suka sheƙa da gudu sai waɗansunsu suka fāɗa cikin ramummukan, sauran kuwa suka gudu zuwa dutsen.
11. Sai abokan gāba suka kwashe dukan kayayyakin Saduma da na Gwamrata, da abincinsu duka, suka yi tafiyarsu.
12. Suka kuma kama Lutu ɗan ɗan'uwan Abram, wanda yake zaune a Saduma, da kayayyakinsa, suka yi tafiyarsu.
13. Sai wani da ya tsere, ya zo ya faɗa wa Abram Ba'ibrane wanda yake zaune wajen itatuwan oak na Mamre, Ba'amore, ɗan'uwan Eshkol da Aner, waɗanda suke abuta da Abram.
14. Lokacin da Abram ya ji an kama danginsa wurin yaƙi sai ya shugabanci horarrun mutanensa, haifaffun gidansa, su ɗari uku da goma sha takwas, suka bi sawun sarakunan har zuwa Dan.