1. A zamanin Amrafel Sarkin Shinar, shi da Ariyok Sarkin Ellasar, da Kedarlayomer Sarkin Elam, da Tidal Sarkin Goyim,
2. suka fita suka yi yaƙi da Bera Sarkin Saduma, da Birsha Sarkin Gwamrata, da Shinab Sarkin Adma, da Shemeber Sarkin Zeboyim, da kuma Sarkin Bela, wato Zowar.
3. Waɗannan sarakuna biyar suka haɗa kai don su kai yaƙi, suka haɗa mayaƙansu a kwarin Siddim, inda Tekun Gishiri take.
4. Shekara goma sha biyu suka bauta wa Kedarlayomer, amma suka tayar a shekara ta goma sha uku.
5. A shekara ta goma sha huɗu Kedarlayomer da sarakunan da suke tare da shi suka zo suka cinye Refayawa cikin Ashterotkarnayim, da Zuzawa cikin Ham, da Emawa cikin Filin Kiriyatayim,
6. da kuma Horiyawa cikin dutsen nan nasu, wato Seyir, har zuwa Elfaran a bakin jeji.
7. Sai suka juya suka je Enmishfat, wato Kadesh, suka kuwa cinye ƙasar Amalekawa da kuma ta Amoriyawa waɗanda suka zauna cikin Hazazontamar.
10. Akwai ramummukan kalo da yawa a kwarin Siddim. Da Sarkin Saduma da na Gwamrata suka sheƙa da gudu sai waɗansunsu suka fāɗa cikin ramummukan, sauran kuwa suka gudu zuwa dutsen.