Ezra 7:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan wannan a zamanin Artashate Sarkin Farisa, sai Ezra ya gane da asalinsa, wato shi na ɗan Seraiya, da Azariya, da Hilkiya,

2. da Shallum, da Zadok, da Ahitub,

3. da Amariya, da Azariya, da Merayot,

4. da Zarahiya, da Uzzi, da Bukki,

5. da Abishuwa da Finehas, da Ele'azara, da Haruna babban firist.

6. Ezra ɗin ya taho daga Babila. Shi malami ne, masanin shari'ar Musa, wadda Ubangiji Allah na Isra'ila ya bayar. Sarki kuwa ya ba shi dukan abin da ya roƙa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.

7. A shekara ta bakwai kuma ta sarautar sarki Artashate, waɗansu mutanen Isra'ila, da waɗansu firistoci, da Lawiyawa,da mawaƙa, da matsaran ƙofa, da ma'aikatan Haikali, suka taho Urushalima.

Ezra 7