1. Haggai kuwa, da Zakariya ɗan Iddo, annabawa, suka yi wa Yahudawan da suke a Yahuza da Urushalima wa'azi da sunan Allah na Isra'ila wanda yake iko da su.
2. Sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozodak, suka tashi suka sāke kama aikin gina Haikalin Allah wanda yake a Urushalima. Annabawan Allah suna tare da su, suna taimakonsu.