Ez 5:9-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Saboda yawan abubuwa masu banƙyama da kika aikata, zan yi miki abin da ban taɓa yi ba, ba kuwa zan sāke yin irinsa ba.

10. Ubanni za su cinye 'ya'yansu, 'ya'ya kuma za su cinye ubanninsu. Zan hukunta ki, waɗanda kuma suka tsira zan watsar da su ko'ina.

11. “‘Tun da yake kin ƙazantar da Haikalina mai tsarki da gumakanki da abubuwanki masu banƙyama, hakika, ni Ubangiji Allah, zan kawar da ke, ba zan ji tausayinki ba, ba kuwa zan haƙura ba.

12. Sulusinki zai mutu da annoba da yunwa. Takobi kuma zai kashe sulusinki, sa'an nan zan watsar da sulusinki ko'ina, zan kuma zare takobi a kansu.

13. “‘Ta haka zan sa fushina ya huce, hasalata kuma a kansu ta lafa, ni kuma in wartsake. Sa'an nan za su sani ni Ubangiji na yi magana da zafin kishi sa'ad da na iyar da fushina a kansu.

14. Zan kuma maishe ki kufai da abin zargi ga al'ummai da suke kewaye da ke, da kuma a idanun dukan masu wucewa.

Ez 5