2. Yankin Ashiru yana kusa da yankin Dan, daga gabas zuwa yamma.
3. Yankin Naftali yana kusa da yankin Ashiru daga gabas zuwa yamma.
4. Yankin Manassa yana kusa da yankin Naftali daga gabas zuwa yamma.
5. Yankin Ifraimu yana kusa da yankin Manassa daga gabas zuwa yamma.
6. Yankin Ra'ubainu yana kusa da yankin Ifraimu daga gabas zuwa yamma.
7. Yankin Yahuza yana kusa da yankin Ra'ubainu daga gabas zuwa yamma.
8. “Kusa da yankin Yahuza daga gabas zuwa yamma, sai yankin da za ku keɓe. Faɗinsa kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], tsawonsa kuma daidai da tsawon yankunan kabilai daga gabas zuwa yamma. Haikali zai kasance a tsakiyar yankin.
9. “Yankin da za ku keɓe wa Ubangiji, tsawonsa zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗinsa kuwa kamu dubu goma [10,000].
10. Wannan tsattsarkan yanki shi ne rabon firistoci. Tsawonsa wajen arewa, kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000] ne, faɗinsa a wajen yamma kuwa, kamu dubu goma [10,000] ne, a wajen gabas faɗinsa kamu dubu goma [10,000], a wajen kudu tsawonsa kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000]. Haikalin Ubangiji zai kasance a tsakiyarsa.
11. Wannan zai zama na keɓaɓɓun firistoci daga zuriyar Zadok waɗanda suka kiyaye umarnina, ba su karkace kamar yadda Lawiyawa suka yi lokacin da jama'ar Isra'ila suka karkace ba.
12. Zai zama rabonsu daga tsattsarkan yankin ƙasar da take kusa da yankin Lawiyawa.