Ez 43:20-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Za ka ɗibi jininsa, ka shafa shi a kan zankaye huɗu na bagaden, da kan kusurwa huɗu na mahaɗin da kan da'irarsa. Ta haka za ka tsarkake bagaden, ka yi kafara dominsa.

21. Za ka kuma ɗauki bijimi na yin hadaya domin zunubi, ka kai shi waje, a wurin da aka shirya a bayan Haikalin, ka ƙone shi.

22. A kan rana ta biyu za ka miƙa bunsuru marar lahani domin yin hadaya don zunubi, bagaden kuma zai tsarkaka, kamar yadda aka tsarkake shi da bijimin.

23. Sa'ad da ka gama tsarkake shi, sai ka miƙa bijimi da rago marar lahani.

24. Za ka kawo su a gaban Ubangiji, firistoci za su barbaɗe su da gishiri, su miƙa su hadayar ƙonawa ga Ubangiji.

Ez 43