Ez 42:15-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sa'ad da ya gama auna cikin Haikalin, ya fito da ni ta ƙofar gabas, sa'an nan ya auna filin da yake kewaye da Haikalin.

16. Ya auna kusurwar gabas da karan awo, kamu ɗari biyar.

17. Sai kuma ya auna kusurwar arewa, kamu ɗari biyar.

18. Kusurwar kudu kamu ɗari biyar.

19. Kusurwar yamma, ita ma kamu ɗari biyar.

Ez 42