19. Duk da haka ta yi ta ƙara karuwancinta, tana tunawa da kwanakin 'yan matancinta, a lokacin da ta yi karuwancinta a ƙasar Masar.
20. Ta yi ta kai da kawowa tsakanin kwartayenta waɗanda al'auransu kamar na jakai ne, maniyyinsu kuwa kamar na dawakai ne.
21. Haka kika yi ƙawar zucin lalatar da kika yi a lokacin 'yan matancinki, sa'ad da Masarawa suka rungumi mamanki na ƙuruciya.”
22. “Domin haka, ya Oholiba, ni, Ubangiji Allah na ce zan kuta kwartayenki su yi gāba da ke, waɗanda kika ji ƙyamarsu, kika rabu da su. Daga kowane sashi zan sa su zo su yi gāba da ke.
23. Babilawa da dukan Kaldiyawa, da Fekod, da Showa, da Kowa, da dukan Assuriyawa tare da su, wato samari masu bansha'awa. Dukansu masu mulki ne, da shugabanni, da jarumawa, da shahararru, dukansu suna kan dawakai.
24. Za su zo daga arewa su yi yaƙi da ke da karusai, da kekunan dawakai, da rundunar mutane. Za su kafa miki sansani a kowace sashi su yi yaƙi da ke da sulke, da garkuwa, da kwalkwali. Zan danƙa shari'a a hannunsu, za su kuwa shara'anta ki da irin shari'arsu.
25. Zan yi fushi da ke don su wulakanta ki. Za su datse hancinki da kunnuwanki. Waɗanda suka rage miki za a kashe su da takobi. Za su kama 'ya'yanki mata da maza, waɗanda suka rage miki kuwa, za a ƙone su da wuta.
26. Za su tsiraita ki, su kuma kwashe lu'ulu'anki.
27. Zan ƙarasa lalatarki da karuwancinki da kika kawo daga ƙasar Masar, don kada ki ƙara ɗaga idonki ki dubi Masarawa, ko ki ƙara tunawa da su.
28. “Gama ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ga shi, zan danƙa ki a hannun waɗanda kike ƙinsu, waɗanda kika ƙi su, kika kuwa rabu da su.
29. Za su nuna miki ƙiyayya, za su ƙwace dukiyarki su bar ki tsirara tik, za su kuma buɗe tsiraicin karuwancinki.
30. Lalatarki da karuwancinki su suka jawo miki wannan, gama kin yi karuwanci da sauran al'umma kika ƙazantar da kanki da gumakansu.
31. Kin bi halin 'yar'uwarki, domin haka zan hukunta ki kamar yadda na hukunta ta.’ ”