1. Sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2. “Ɗan mutum, akwai waɗansu mata biyu, uwarsu ɗaya.
3. Sun yi karuwanci a Masar, a lokacin 'yan matancinsu, aka rungumi mamansu da ƙirjinsu.
4. Sunan babbar Ohola, sunan ƙanwar kuwa Oholiba. Sun zama nawa, sun haifi 'ya'ya mata da maza. A kan sunayensu kuwa Ohola ita ce Samariya, Oholiba kuwa ita ce Urushalima.
5. Ohola ta yi karuwanci sa'ad da take zamana. Ta yi ta kai da kawowa a tsakanin kwartayenta, Assuriyawa,
6. waɗanda suke saye da shunayya, su masu mulki da manyan sojoji, dukansu samari ne masu bansha'awa, suna bisa kan dawakansu.
7. Ta yi karuwanci da su, dukan waɗanda suke ƙusoshin Assuriya, ta kuma ƙazantar da kanta tsakanin gumakan da ta yi ta kai da kawowa a cikinsu.