45. Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,
46. “Ɗan mutum, ka fuskanci wajen kudu ka ja kunnen mutanen kudu, ka kuma yi annabci gāba da kurmin ƙasar Negeb.
47. Ka ce wa kurmin Negeb, ‘Ka ji maganar Ubangiji, gama Ubangiji Allah ya ce zai kunna wuta a cikinka, za ta kuwa cinye kowane ɗanyen itace, da kowane busasshen itacen da take cikinka. Ba za a kashe harshen wutar ba. Harshen wutar zai babbake kowace fuska daga kudu zuwa arewa.
48. Dukan masu rai za su sani ni Ubangiji ne na kunna wutar, ba wanda zai kashe ta.”’
49. Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, suna cewa misalai kawai, nake yi.”