20. Wanda ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai ɗauki hakkin laifin mahaifinsa ba, mahaifi kuma ba zai ɗauki hakkin laifin ɗansa ba. Adalcin adali nasa ne, muguntar mugu kuma tasa ce.
21. “Amma idan mugu ya bar dukan muguntarsa da ya aikata, ya kiyaye dokokina, ya bi shari'a, ya yi abin da yake daidai, zai rayu, ba zai mutu ba.
22. Ba za a bi hakkin laifin da ya aikata ba. Zai rayu saboda adalcin da ya yi.
23. Ni Ubangiji Allah, na ce, ina jin daɗin mutuwar mugu ne? Ban fi so ya bar mugun halinsa ya rayu ba?
24. “Amma idan adali ya bar yin adalci, ya aikata mugunta, ya yi abubuwa masu banƙyama waɗanda mugu yake aikatawa, zai rayu? Ayyukansa na adalci waɗanda ya aikata, ba za a tuna da su ba, faufau. Zai mutu saboda rashin amincin da ya yi da laifin da ya aikata.
25. “Amma kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ku ji ya ku mutanen Isra'ila, hanyata ba daidai ba ce? Ashe, ba hanyarku ce ba daidai ba?
26. Sa'ad da adali ya bar adalcinsa, ya kuwa aikata mugunta zai mutu saboda muguntarsa.