Ez 13:9-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ikona zai yi gāba da annabawan da suke ganin wahayin ƙarya, waɗanda suke kuma yin duban ƙarya. Ba za su kasance cikin taron mutanena ba, ba kuwa za a rubuta su a littafin mutanen Isra'ila ba, ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Za ku kuwa sani, ni ne Ubangiji Allah.

10. “Domin sun ɓad da mutanena suna cewa, ‘Salama,’ sa'ad da ba salama, sa'ad da kuma mutanen suke gina garu marar aminci, sai annabawan nan su shafe shi da farar ƙasa,

11. ka faɗa wa waɗanda suka shafe garun da farar ƙasa, cewa zai faɗi. Za a yi rigyawa da ƙanƙara, da babban hadiri mai iska.

12. Sa'ad da garun ya faɗi, ashe, ba za a tambaye ku ba cewa, ‘Ina shafen farar ƙasar da kuka yi masa?’

13. “Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce da hasalata zan sa babban hadiri mai iska, da rigyawa, da manyan ƙanƙara su hallaka shi.

14. Zan rushe garun da kuka shafe da farar ƙasa. Za a baje shi, a bar tushen a fili. Za ku halaka a tsakiyarsa sa'ad da ya fāɗi, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.

15. “Ta haka zan aukar da hasalata a kan garun, da a kan waɗanda suka shafe shi da farar ƙasa. Sa'an nan zan faɗa muku, cewa garun ya faɗi tare da waɗanda suka shafe shi da farar ƙasa.

16. Wato annabawan Isra'ila waɗanda suka yi annabci a kan Urushalima, suka ga wahayin salama dominta, ga shi kuwa, ba salama, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

17. “Kai kuwa ɗan mutum, sai ka ɗaure wa matan mutanenka fuska, waɗanda suke annabci bisa ga son zuciyarsu. Ka yi annabci a kansu,

18. ka ce, ‘Ubangiji Allah ya ce, kaiton matan da suke ɗinka wa mutane kambuna, suna yi wa mutane rawunan dabo bisa ga zacinsu don su farauci rayukan mutane. Za ku farauci rayukan mutanena, sa'an nan ku bar rayukan waɗansu don ribar kanku?

Ez 13