17. “Kai kuwa ɗan mutum, sai ka ɗaure wa matan mutanenka fuska, waɗanda suke annabci bisa ga son zuciyarsu. Ka yi annabci a kansu,
18. ka ce, ‘Ubangiji Allah ya ce, kaiton matan da suke ɗinka wa mutane kambuna, suna yi wa mutane rawunan dabo bisa ga zacinsu don su farauci rayukan mutane. Za ku farauci rayukan mutanena, sa'an nan ku bar rayukan waɗansu don ribar kanku?
19. Kun saɓi sunana a cikin mutanena don a tafa muku sha'ir, a ba ku ɗan abinci. Kuna kashe mutane waɗanda bai kamata su mutu ba, kuna barin waɗanda bai kamata su rayu ba ta wurin ƙaryace-karyacen da kuke yi wa mutanena waɗanda suke kasa kunne ga ƙaryace-ƙaryacen.’
20. “Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce, ina gāba da kambunanku da kuke farautar rayuka da su. Zan tsintsinke su daga damatsanku, in saki rayuka waɗanda kuka farauto kamar tsuntsaye.