Ez 12:4-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Za ka fitar da kayanka da rana a kan idonsu, kamar kayan mai tafiyar zaman talala. Kai kuma da kanka za ka tafi da maraice a kan idonsu, kamar yadda mutane masu tafiyar zaman talala sukan yi.

5. Ka huda katanga a kan idonsu, sa'an nan ka fita daga ciki.

6. A gabansu za ka ɗauki kayan, ka saɓa shi a kafaɗarka, ka tafi da shi da dare. Za ka rufe fuskarka don kada ka ga ƙasar, gama na maishe ka alama ga jama'ar Isra'ila.”

7. Na kuwa yi kamar yadda aka umarce ni. Na fitar da kayana da rana, kamar kayan mai tafiyar zaman talala. Da maraice na huda katanga da hannuwana, sa'an nan na fita da duhu, ina ɗauke da kayana a kafaɗa, a kan idonsu.

8. Da safe kuwa Ubangiji ya yi mini magana, ya ce,

9. “Ɗan mutum, ashe, mutanen Isra'ila, 'yan tawayen nan, ko suka ce maka, ‘Me kake yi?’

10. Ka ce musu, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Wannan jawabi ya shafi shugabannin Urushalima da dukan mutanen Isra'ila, waɗanda suke cikinta.’

11. Ka ce musu, ‘Ni alama ne a gare ku, kamar yadda na yi, haka za a yi da ku, za a kai ku bauta.’

12. Sarkin da yake cikinsu zai ɗauki kayansa ya saɓa a kafaɗarsa, ya fita da duhu. Zai huda katanga ya fita. Zai rufe fuskarsa don kada ya ga ƙasar da idanunsa.

13. Zan yarɓa masa ragata in kama shi. Zan kai shi Babila, wato ƙasar Kaldiyawa, duk da haka ba zai gan ta ba, ko da yake zai rasu a can.

14. Zan warwatsa dukan waɗanda suke kewaye da shi, masu taimakonsa da sojojinsa ko'ina. Zan zare takobi in runtume su.

15. “Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na watsa su cikin sauran al'umma da cikin ƙasashe.

Ez 12