1. Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2. “Ɗan mutum, kana zaune a tsakiyar gidan 'yan tawaye da suke da idanun gani, amma ba sa gani, suna da kunnuwa na ji, amma ba sa ji, gama su 'yan tawaye ne.
3. Domin haka, ɗan mutum sai ka shirya kaya don zuwa zaman talala, sa'an nan ka tashi da rana a kan idonsu. Za ka ƙaura daga wurinka zuwa wani wuri a kan idonsu, watakila za su gane, cewa su 'yan tawaye ne.
4. Za ka fitar da kayanka da rana a kan idonsu, kamar kayan mai tafiyar zaman talala. Kai kuma da kanka za ka tafi da maraice a kan idonsu, kamar yadda mutane masu tafiyar zaman talala sukan yi.
5. Ka huda katanga a kan idonsu, sa'an nan ka fita daga ciki.