Esta 4:3-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. A kowane lardi inda aka kai umarni da dokar sarki, Yahudawa suka yi babban baƙin ciki, da azumi, da kuka, da makoki. Waɗansu da yawa da rigunan makoki a cikin toka suka kwanta.

4. Sa'ad da kuyangin Esta da bābāninta suka tafi suka faɗa mata abin da Mordekai yake yi, sai sarauniya Esta ta damu ƙwarai, ta aika da riguna a sa wa Mordekai, ya tuɓe rigar makokinsa, amma Mordekai ya ƙi, bai yarda ba.

5. Sai Esta ta kirawo Hatak, ɗaya daga cikin bābānin sarki, wanda aka sa ya yi mata hidima, ta aike shi wurin Mordekai, don ya ji abin da ya faru, har ya sa yake yin haka.

6. Hatak kuwa ya tafi wurin Mordekai a dandalin birnin, a gaban ƙofar sarki.

7. Sai Mordekai ya faɗa masa dukan abin da ya faru da shi, da yawan ƙudin da Haman ya ce zai biya a sa a baitulmalin sarki don a hallaka Yahudawa.

8. Mordekai kuma ya ba Hatak takardar dokar da aka yi a Shushan don a hallaka Yahudawa domin ya tafi ya nuna wa Esta ya sanar da ita, ya kuma umarce ta ta tafi wurin sarki don ta roƙi arziki ga sarki saboda mutanenta.

9. Sai Hatak ya tafi, ya faɗa wa Esta abin da Mordekai ya ce.

10. Esta kuma ta yi magana da Hatak sa'an nan ta aike shi da saƙo a wurin Mordekai cewa,

Esta 4