25. Zai yi maganganun saɓo a kan Maɗaukaki, zai tsananta wa tsarkaka na Maɗaukaki, zai yi ƙoƙari ya sāke lokatai, da shari'a, za a kuwa bashe su a hannunsu, har shekara uku da rabi.
26. Amma majalisa za ta zauna ta yanke shari'a, za a karɓe mulkinsa, a hallaka shi har abada.
27. Sa'an nan za a ba da sarauta da girman dukan mulkokin duniya ga tsarkaka na Maɗaukaki. Mulkinsa madawwamin mulki ne. Dukan sarakunan duniya za su bauta masa, su kuma yi masa biyayya.’
28. “Ni Daniyel na firgita ƙwarai, fuskata ta yi yaushi. Amma na riƙe al'amarin duka a zuciyata.”