1. Nebukadnezzar ya yi mafarki a shekara ta biyu ta sarautarsa, ya kuwa damu ƙwarai har barci ya gagare shi.
2. Sai sarki ya umarta a kirawo masa masu sihiri, da masu dabo, da bokaye, da Kaldiyawa, su zo su fassara masa mafarkin da ya yi. Sai suka hallara a gaban sarki.
3. Sarki kuwa ya ce musu, “Na yi mafarki, na kuwa matsu ƙwarai in san mafarkin.”
4. Sai Kaldiyawa suka yi magana da sarki da Aramiyanci, suka ce, “Ran sarki ya daɗe! Ka faɗa wa barorinka mafarkin, za mu kuwa yi maka fassararsa.”