Dan 1:5-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sarki kuwa ya sa a riƙa ba su abinci da ruwan inabi irin nasa kowace rana. A kuma koyar da su har shekara uku. Bayan shekara uku za su shiga yi wa sarki hidima.

6. A cikin waɗanda aka zaɓa akwai Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya, daga kabilar Yahuza.

7. Sai sarkin fāda ya laƙaba musu sababbin sunaye. Ya kira Daniyel, Belteshazzar, ya kira Hananiya, Shadrak, ya kira Mishayel, Meshak, sa'an nan ya kira Azariya, Abed-nego.

8. Daniyel kuwa ya ƙudura a ransa, ba zai ƙazantar da kansa da cin abinci iri na sarki da shan ruwan inabinsa ba, don haka ya roƙi sarkin fāda, kada ya ba shi wannan abincin da zai ƙazantar da shi.

9. Allah kuwa ya sa Daniyel ya sami farin jini da soyayya a wurin sarkin fāda.

10. Sa'an nan sarkin fāda ya ce wa Daniyel, “Ina jin tsoro kada shugaban sarki wanda ya umarta a riƙa ba ku wannan abinci da ruwan inabi ya ga jikinku ba su yi kyau kamar na samarin tsaranku ba, ta haka za ku sa in shiga uku a wurin sarki.”

11. Sai Daniyel ya ce wa baran da sarkin fāda ya sa ya lura da su Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya,

Dan 1