Dan 1:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sa'an nan Sarkin Babila ya umarci sarkin fādarsa, Ashfenaz, ya zaɓo masa waɗansu samari daga cikin Yahudawa, waɗanda suke daga gidan sarauta, da kuma daga gidan manya,

4. su kasance samari ne kyawawa, waɗanda ba su da wata naƙasa, masu fasaha cikin kowane abu, masu fahimta, da masu saurin ganewa, waɗanda suke da halin iya hidima a fādar sarki. Nebukadnezzar ya umarci Ashfenaz ya koya musu littattafan Kaldiyawa da harshen Kaldiyawa.

5. Sarki kuwa ya sa a riƙa ba su abinci da ruwan inabi irin nasa kowace rana. A kuma koyar da su har shekara uku. Bayan shekara uku za su shiga yi wa sarki hidima.

6. A cikin waɗanda aka zaɓa akwai Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya, daga kabilar Yahuza.

7. Sai sarkin fāda ya laƙaba musu sababbin sunaye. Ya kira Daniyel, Belteshazzar, ya kira Hananiya, Shadrak, ya kira Mishayel, Meshak, sa'an nan ya kira Azariya, Abed-nego.

8. Daniyel kuwa ya ƙudura a ransa, ba zai ƙazantar da kansa da cin abinci iri na sarki da shan ruwan inabinsa ba, don haka ya roƙi sarkin fāda, kada ya ba shi wannan abincin da zai ƙazantar da shi.

Dan 1