Dan 1:13-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sa'an nan ka duba fuskokinmu da na samari waɗanda suke cin abinci irin na sarki. Ka yi da barorinku gwargwadon yadda ka gan mu.”

14. Ya yarda da abin da Daniyel ya ce, ya kuwa jarraba su har kwana goma ɗin.

15. A ƙarshen kwana goma ɗin, sai aka ga fuskokinsu suna sheƙi, sun kuma yi ƙiba fiye da samarin da suke cin abinci irin na sarki.

16. Don haka baran ya janye shirin ba su abinci da ruwan inabi irin na sarki, ya ci gaba da ba su kayan lambu.

17. Waɗannan samari huɗu kuwa, Allah ya ba su ilimi, da sanin littattafai, da hikima. Ya kuma yi wa Daniyel baiwar ganewar wahayi da mafarkai.

18. Sa'ad da lokacin da sarki ya ƙayyade ya ƙare, sarkin fāda ya gabatar da su a gaban Nebukadnezzar.

Dan 1