Ayu 39:20-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Kai ne ka sa shi tsalle kamar ɗango?Kwarjinin firjinsa yana da bantsoro.

21. Yakan yi nishi a fadama,Yana murna saboda ƙarfinsa,A wurin yaƙi ba ya ja da baya, ba ya jin tsoron kibau.

22. Tsoro abin dariya ne a gare shi, bai damu ba.Ba ya ba da baya ga takobi,

23. Kibau na ta shillo a kansa,Māsu suna ta gilmawa a gabansa.

24. Da tsananin fushi da hasala yana kartar ƙasa,Da jin ƙarar ƙaho, sai ya yi ta zabura.

25. Sa'ad da aka busa ƙaho yana ce, ‘Madalla.’Yakan ji warin yaƙi daga nesa, da hargowar sarakunan yaƙi da ihunsu.

26. “Ta wurin hikimarka ne shirwa take tashi,Ta buɗe fikafikanta ta nufi kudu?

27. Ta wurin umarninka ne gaggafa take tashi samaTa yi sheƙarta can ƙwanƙoli?

28. A kan dutse take zaune, a can take gidanta,Cikin ruƙuƙin duwatsu.

29. Daga can takan tsinkayi abincintaIdanunta sukan hango shi tun daga nesa.

30. 'Yayanta sukan tsotsi jini,A inda kisassu suke, can take.”

Ayu 39