Ayu 3:20-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. “Me ya sa ake barin mutane su yi ta zama cikin damuwa?Me ya sa ake ba da haske ga waɗanda suke baƙin ciki?

21. Sun jira mutuwa, amma ta ƙi samuwa,Sun fi son kabari da kowace irin dukiya.

22. Ba su da farin ciki, sai sun mutu an binne su tukuna.

23. Allah ya ɓoye musu sanin abin da zai faru nan gaba,Ya kalmashe su kowane gefe.

Ayu 3