Ayu 2:11-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Sa'ad da uku daga cikin abokan Ayuba, wato Elifaz daga birnin Teman, da Bildad daga ƙasar Shuwa, da Zofar daga ƙasar Na'ama, suka ji labarin irin yawan wahalar da Ayuba yake sha, sai suka kama hanya suka tafi su ziyarce shi, su ta'azantar da shi.

12. Suka hango Ayuba tun daga nesa, amma ba su gane shi ba. Da suka gane shi sai suka fara kuka da murya mai ƙarfi. Suka kyakkece tufafinsu saboda baƙin ciki, suka ɗibi ƙura suka watsa a kawunansu.

13. Sa'an nan suka zauna a ƙasa tare da shi, har kwana bakwai, amma ba wanda ya ce uffan, saboda ganin irin yawan wahalar da yake sha.

Ayu 2