16. Allah mai iko ne a kullum kuwa cikin nasara yakeDa macuci, da wanda aka cutar, duk ƙarƙashin ikon Allah suke.
17. Yakan mai da hikimar masu mulki wauta,Yakan mai da shugabanni marasa tunani.
18. Yakan tuɓe sarakuna ya sa su kurkuku.
19. Yakan ƙasƙantar da firistoci da mutane masu iko.
20. Yakan rufe bakin waɗanda aka amince da su.Yakan kawar da hikimar tsofaffi.
21. Yakan kunyatar da masu iko,Ya hana wa masu mulki ƙarfi.
22. Yakan aika da haske a wuraren da suke da duhu kamar mutuwa.
23. Yakan sa sauran al'ummai su yi ƙarfi su ƙasaita,Sa'an nan ya fatattaka su, ya hallaka su.