5. Ubangiji Allah Mai RundunaYa taɓi duniya, ta girgiza.Duk waɗanda suke zaune cikintaSuna baƙin ciki.Duniya duka takan hauTa kuma gangara kamar ruwanKogin Nilu.
6. Ubangiji ya gina al'arshinsa a sama,Ya shimfiɗa samaniya a bisa duniya.Ya sa ruwan teku ya zo,Ya kwarara shi a bisa duniya.Sunansa Ubangiji ne!
7. Ubangiji ya ce, “Jama'ar Isra'ila,Ina yi da ku daidai yadda nake yi daHabashawa.Na fito da Filistiyawa daga Kaftor,Suriyawa kuwa daga Kir,Daidai yadda na fito da ku dagaMasar.