1. Na ga Ubangiji na tsaye a wajen bagade. Ya yi umarni, ya ce,“Bugi ginshiƙan Haikali don shirayiduka yă girgiza.Farfasa su, su fāɗi a kan mutane!Sauran mutane kuwa,Zan kashe su a wurin yaƙi.Ba wanda zai tsere, ko ɗaya.
2. Ko da za su nutsa zuwa lahira,Zan kama su.Ko sun hau Sama,Zan turo su.