Amos 5:8-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ubangiji ne ya yi taurarinKaza da 'ya'yantaDa mai farauta da kare.Ya mai da duhu haske,Rana kuwa dare.Shi ya kirawo ruwan teku yabayyana,Ya shimfiɗa shi a bisa ƙasa.Sunansa Ubangiji ne.

9. Ya kawo halaka a kan ƙarfafa,Da a kan birane masu garu.

10. Kun ƙi wanda ya tsaya a kanadalci,Da mai faɗar ainihin gaskiya a gabanshari'a.

11. Kun matsa wa talakawa lamba,Kun ƙwace musu abincinsu.Saboda haka kyawawan gidajen nanda kun gina da dutse,Ba za ku zauna a cikinsu ba,Ba kuwa za ku sha ruwan inabinnanDaga kyawawan gonakin inabinkuba.

12. Na san irin zunuban da kuke yi,Da mugayen laifofin da kuka aikata.Kuna wulakanta mutanen kirki,Kuna cin hanci,Kuna hana a yi wa talakawa shari'aradalci a majalisa.

13. Ashe, ba abin mamaki ba ne,Da masu hankali suka kame bakinsuA waɗannan kwanaki na mugunta.

Amos 5