A.m. 28:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan da muka tsira, sai muka ji, ashe, sunan tsibirin nan Malita ne.

2. Mutanen garin kuwa sun yi mana alheri matuƙar alheri, don sun hura wuta sun karɓe mu, mu duka, saboda ana ruwa, ga kuma sanyi.

3. Sa'ad da Bulus ya tattaro waɗansu ƙirare rungume guda ya sa a wutar, sai ga wani maciji ya bullo saboda zafi, ya ɗafe masa a hannu.

4. Da mutanen garin suka ga mugun ƙwaron nan a makale a hannun Bulus, suka ce wa juna, “Lalle mutumin nan mai kisankai ne, kun ga ko da yake ya tsira daga bahar, duk da haka alhaki yana binsa sai ya mutu.”

5. Bulus kuwa ya karkaɗe ƙwaron a cikin wutar, bai kuwa ji wani ciwo ba.

6. Su kuwa suna zaton wurin zai kumbura, ko kuwa farat ɗaya ya fāɗi matacce. Amma da aka daɗe suka ga ba abin da ya same shi, suka sāke magana suka ce lalle shi wani Allah ne.

A.m. 28