A.m. 25:24-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Sai Festas ya ce, “Ya sarki Agaribas, da dukan mutanen da suke tare da mu, kun ga mutumin nan da duk jama'ar Yahudawa suka kawo mini ƙararsa a Urushalima, da kuma nan, suna ihu, bai kamata a bar shi da rai ba.

25. Amma ni ban ga abin da ya yi wanda ya isa kisa ba. Tun da kuma shi kansa ya nema a mai da shari'arsa a gaban Augustas, ƙudura in aika da shi zuwa wurinsa.

26. Amma ba ni da wata tabbatacciyar magana da zan rubuta wa ubangijina game da shi. Saboda haka na kawo shi a gabanku, musamman kuwa a gabanka, ya sarki Agaribas, don bayan an yi bincike, ko na abin da zan rubuta.

27. Don ni, a ganina, wauta ce a aika da ɗan sarƙa, ba tare da an nuna laifofin da ya yi ba.”

A.m. 25