A.m. 23:33-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. Da baraden suka isa Kaisariya, suka ba mai mulkin wasiƙar, suka kai Bulus a gabansa.

34. Da ya karanta wasiƙar, ya tambayi Bulus ko shi mutumin wane lardi ne? Da ya ji daga Kilikiya yake,

35. ya ce, “Zan saurari maganarka duka, in masu ƙararka sun zo.” Sai kuma ya yi umarni a tsare shi a fadar Hirudus.

A.m. 23