A.m. 23:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Bulus ya zuba wa majalisar ido ya ce, “Ya ku 'yan'uwa, bautar Allah nake yi da lamiri mai kyau har ya zuwa yau.”

2. Sai Hananiya babban firist ya umarci waɗanda suke tsaye kusa da Bulus su buge bakinsa.

3. Sai Bulus ya ce masa, “Kai munafiƙi, kai ma Allah zai buge ka! Ashe, wato kana zaune kana hukunta ni bisa ga Shari'a ne, ga shi kuwa kana yin umarni a doke ni, a saɓanin Shari'a?”

A.m. 23