A.m. 12:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A lokacin nan kuwa sarki Hirudus ya fara gwada wa waɗansu 'yan Ikkilisiya tasku,

2. har ma ya sare Yakubu ɗan'uwan Yahaya da takobi.

3. Da ya ga abin ya ƙayatar da Yahudawa, har wa yau kuma ya kama Bitrus, shi ma. Kwanakin idin abinci marar yisti ne kuwa.

A.m. 12