2 Tim 4:17-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya ba ni ƙarfin sanar da bishara sosai da sosai, domin duk al'ummai su ji, aka kuwa cece ni daga bakin zaki.

18. Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun abu, ya kuma kiyaye ni, ya kai ni ga Mulkinsa na Sama. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!

19. Ka gayar mini da Bilkisu da Akila, da mutanen gidan Onisifaras.

20. Aratas ya dakata a Koranti. Tarofimas kuwa na bar shi a Militas, ba shi da lafiya.

21. Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo kafin damuna. Aubulus yana gaishe ka, da Budis, da Linas, da Kalaudiya, da kuma dukkan 'yan'uwa.

22. Ubangiji yă kasance a zuciyarka. alheri yă tabbata a gare ku.

2 Tim 4