2 Tim 1:5-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ina tunawa da sahihiyar bangaskiyarka, wadda da farko take tare da kakarka Loyis, da mahaifiyarka Afiniki, a yanzu kuma na tabbata tana tare da kai.

6. Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwar nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗora maka hannuwana.

7. Ai, Allah ba halin tsoro ya ba mu ba, hali mai ƙarfi ne, mai ƙauna, da kuma kamunkai.

8. Saboda haka, kada ka ji kunyar ba da shaidar Ubangijinmu, da kuma tawa, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi, sai dai mu jure wa shan wuya tare, saboda bishara, bisa ga ikon Allah,

9. wanda ya cece mu, ya kuma kira mu da kira mai tsarki, ba don wani aikin lada da muka yi ba, sai dai domin nufinsa, da kuma alherinsa, da aka yi mana baiwa tun fil'azal, a cikin Almasihu Yesu,

2 Tim 1